✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta amince a bude cibiyoyi 774 na sabunta layin waya

Za a bude wurare 774 na sabunta layukan waya domin saukaka rajista da samun lambar NIN Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta amince da kafa cibiyoyi 774 na  sabunta layukan waya domin saukaka rajista da kuma samun lambar kasa ta NIN a fadin Najeriya.

Ta kuma amince da tsawaita lasisin kamfanonin sadarwa da ke yin aikin rajistar daga daya zuwa shekaru biyar.

Kwamitin hadin gwiwa da Ministan Sadarwa kan hada layukan waya da lambar NIN ne ya sanar da haka a ranar Laraba.

Kwamitin ya kuma ba da umarnin kammala aikin sabon tsarin bayar sa sabbin layukan waya da babu ha’inci a ciki.

“Wannan zai tabbatar da cewa ba a maimaita abin da aka yi a baya ba wanda aka samu matsala ta hanyar rajista da wasu wakilai”, inji sanarwar kwamitin.

Sanarwar ta ce, “An amince da tsawaita wa’adin lasisin rajistar NIN na wakilcin daga shekara 1 zuwa 5 ne bayan gamsuwa da aikin kamfanonin kuma za ci gaba da sa ido a kan.

“Wannan yunkurin gwamnati ne saukaka yin rajista ga yan Nijeriya da kuma halastattun baku,’’ inji sanarwar.