✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta ba da hutun Karamar Sallah

Za a yi hutun a ranakun Laraba da Alhamis domin bikin Karamar Sallar.

Gwanmatin Tarayya ta ayyana ranakun Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutu domin bikin Karamar Sallar bana.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya sanar da hakan a ranar Litinin.

“Laraba 12 da Alhamis, 13 ga Mayu, 2021 su ne ranakun hutun da Gwamnatin Tarayya ta bayar domin bukukuwan Sallah Karama a bana,” inji sanarwar.

Aregbesola ya taya Musulmin murnar zuwan Sallar, sannan ya kara da kiran ’yan Najeriya a gida da kasashen waje da su dage wajen yi wa kasar addu’ar samun zaman lafiya da karuwar arziki.

Tuni Mai Alfarma, Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar cewa a ranar Talata za a fara neman watan Shawwal na Karamar Sallah.

Ranar Talata 11 ga Mayu 2021, ita ce 29 ga watan Ramadan 1442 Hijiriyya.