✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta ba da tabbacin kawo karshen yajin aikin ASUU

Shugaban kasa ya bani umarnin cewa duk rintsi na tabbatar an janye yajin aikin.

Gwamnatin Tarayya ta bayar da tabbacin kawo karshen yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU, da ya ki ci ya cinyewa, inda a baya-bayan nan ta kwashe tsawon watanni bakwai tana yi.

Ministan Kwadago da Samar da Aiki, Sanata Chris Ngige ne ya bayyana haka da Yammacin ranar Litinin, a wani zama na ci gaba da sulhu tsakanin Gwamnati da kungiyar ta ASUU, da ya gudana a dakin taro na Ma’aikatar Kwadago da Samar da Aiki.

Ngige ya ce “Shugaban kasa ya bani umarnin cewa duk rintsi kada na yi kasa a gwiwa har sai na tabbatar an tattauna komai don kawo karshen zaman gida da dalibai suka jima suna yi ba tare da sun je makaranta ba, na kuma tabbatar an janye yajin aikin.”

“Ya kuma bani umarnin na bude kofar samar da daidaito ta yadda kowane bangare zai hakura da abin da ya samu don samar da maslaha.”

“Hakika kudaden da Gwamnati ke samu a matakin tarayya ya ja baya kafin zuwan wannan gwamnati.”

Ministan ya ce, “Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana cike da damuwa kwarai da gaske a kan halin da jami’o’in kasar nan ke ciki, yana kuma iya bakin kokarinsa don kawo karshen matsalolin.”

Ministan ya ci gaba da cewa “Shugaban kasa ya tabbatar min cewa ya kudurce a ransa zai yi iya iyawarsa don ganin ya farfado da jami’o’inmu ta hanyar tunkarar kalubalen da manyan makarantun ilimi ke ciki a kasar nan, don ganin ya zama tarihi.”