✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta ba dan kwangila wata 4 ya kammala aikin titi a Kano

Ministan ya koka kan yadda ya ce aikin na tafiyar hawainiya

Gwamnatin Tarayya ta ba kamfanin gine-gine na Dantata & Sawoe wa’adin nan da karshen watan Disamban 2022 ya kammala aikin titin Western Bypass da ke birnin Kano.

Minista a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Umar Ibrahim EL-Yakub ne ya ba da wa’adin ranar Asabar, lokacin da yake duba aikin titin mai tsawon kilomita 26.6.

Ya koka kan yadda ya ce aikin na tafiyar hawainiya, inda ya ce ya zama wajibi kamfanin ya kammala shi nan da karshen shekarar da muke ciki.

Ministan ya ce, “A zahirin gaskiya wannan aikin yana tafiyar hawainiya. Saboda haka, na ba wannan kamfanin nan da karshen watan Disamba ya kammala shi. Dole ne a kammala wannan aikin kafin wa’adin gwamnatin Buhari ya kare.

“Za mu samar da dukkan kudaden da ake bukata ga aikin don tabbatar da ba mu bar kowanne aikin da muka fara ba kafin karewar wa’adin gwamnatinmu,” inji shi.

Tun da farko, Injiniyan da ke kula da aikin, Kasimu Maigwandu, ya koka da yadda ya ce tashin farashin kayayyaki, musamman ma na man dizal ne babban kalubalensu a aikin.

Sai dai ya ce tuni suka kammala kaso 71.18 cikin 100 na aikin, kuma suna da kwarin gwiwar kammala ragowar kafin wa’adin da aka ba su ya cika.

Aikin titin dai wanda ya fara tun daga Na’ibawa a kan hanyar Kano zuwa Kaduna kuma ya kare a garin Dawanau da ke hanyar Kano zuwa Katsina an bayar da shi ne tun a shekarar 2007 bisa yarjejeniyar kammalawa cikin shekara uku, kafin daga bisani gwamnatin Buhari ta sabunta tare da kara wa’adin kwangilar.

Kazalika, Minista EL-Yakub ya duba aikin titin Kano zuwa Gwarzo zuwa Dayi, inda ya ce Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar jihohin Kano da Katsina, wadanda aikin ya shafa sun kammala yarjejeniyar biyan diyyar da take yi wa aikin tarnaki.

A wani labarin kuma, Ministan ya ce gwamnatin Shugaba Buhari ya zuwa yanzu ta kammala aikin gina gidaje sama da 2,600 daga cikin guda 5,946 da ta fara a jihohi 35 da Abuja.

Ministan ya bayyana hake ne lokacin da yake duba rukunin farko na gidajen da Gwamnatin Tarayya ta gina a unguwar Jaba da ke birnin Kano.

Ya ce, “Wannan aikin ya zo daidai da yunkurin gwamnatin Buhari na samar da gidaje masu sauki ga ’yan kasa. Za a iya mallakar gidajen ko dai ta hanyar saye kai tsaye ko ta adashin gata ko kuma ya hanyar biya sannu a hankali.”

Minista EL-Yakub ya kuma ce bisa kiyasinsu, ayyukan gina gidajen sun samar wa mutum sama da 70,000 ayyukan yi, wanda ya ce suna amfanar ba iya wadanda za su mallake su ko ’yan kwangila kawai ba, har ma da habakar tattalin arzikin kasa.