✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta ciri biliyan N57 daga CBN a asirce —Majalisa

Majalisa ta bankado yadda aka ciri Naira biliyan 75daga Babban Bankin Najeriya a asirce.

Majalisar Dattawa ta bankado yadda aka ciri Naira biliyan 7 da miliyan 500 daga Babban Bankin Najeriya (CBN) a asirce.

Majalisar Dattawa ta bukaci Ministar Kudi, Zainab Ahmed da Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris, su bayyana a gabanta domin warware zare da abawa kan kudaden da aka cira a asirce.

“Naira biliyan 3.84, Akanta-Janar na Tarayya da Ma’ikatar Kudi ta Kasa ne suka cire su ba bisa ka’ida ba daga CBN… a matsayin rance domin sayen motoci ga jami’an tsaro a 2005 da 2006,” inji Majalisar a wani bangare na rahotonta.

Rahoton binciken da Kwamitin Asusun Gwamnati na Majalisar ya gudanar ya ce an zari kudaden ne a lokuta daban-daban daga asusn Hukumar Kera Motoci ta Kasa daga shekarar 2000 zuwa 2006.

Amma da ta nemin karin bayani daga Darakta-Janar na Hukumar, Aminu Jalal, ya ce ba su da masaniya game da cirar kudaden.

Ya ce Hukumar ta sha rubuta wa Akanta-Janar na Kasa tana neman a dawo mata da kudaden amma hakarta ba ta cimma ruwa ba.

Da jin haka ne Majalisar Dattawa ta umarci Akanta-Janar din tare da Ministar Kudi, Zainab Ahmed su bayyana a gabanta domin su yi bayani.