✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnati ta fara ‘tattaunawa’ da wadanda suka sace fasinjojin jirgin kasan Kaduna

Lamarin na zuwa ne bayan cikar wa’adin da iyalan mutanen suka ba gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta fara ‘tattaunawa’ da ’yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sama da 60 mako biyu da suka wuce, kamar yadda iyalan wadanda aka sace suka tabbatar.

Akalla mutum tara ne aka ba da rahoton kashe su, sama da 60 kuma aka yi awon gaba da su bayan kai harin bam a kan jirgin.

Da suke zantawa da manema labarai a Kaduna ranar Juma’a, iyalai da abokan wadanda aka sace din sun ce Gwamnatin Tarayya ta ba su tabbacin cewa ta bude kofofin tattaunawa da ’yan ta’addan.

“Bayan taron Majalisar Zartarwa ta Kasa ranar Laraba, mun ji cewa Gwamnatin Tarayya, ta bakin Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed cewa an fara tattaunawar da wadanda suka sace mana ’yan uwa,” inji Dokta Jimoh Fatai, wani wanda aka nada a matsayin Shugaban masu fafutukar ganin an sako mutanen.

“Muna murna da hakan, mun ji dadi kuma muna godiya da kulawar gwamnatin a kan haka. Abin da kawai muke roko a yanzu shi ne gwamnatin ta hanzarta aikin,” inji shi.

Aminiya ta rawaito cewa labarin na zuwa ne bayan cikar wa’adin sa’o’i 72 da iyalan mutanen suka ba gwamnatin na ta fara tattaunawar.

Sai dai Dokta Jimoh ya ce tun bayan tuntubar farko da ’yan ta’addan suka yi musu suka shaida musu sune suka sace mutanen, har yanzu ba su sake kiransu ba.

Ya ce ’yan uwan nasu na cikin mawuyacin hali kuma suna tsananin bukatar taimako, musamman ganin yadda damina ke dada karatowa.

Shugaban ya kuma shawarci Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya kan kada ta kuskura ta dawo da sufurin jiragen Abuja zuwa Kaduna, inda suka ce a maimakon haka kamata ya yi ta fi mayar da hankali wajen ceto mutanen da aka sace.