✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta fito da Abinci ta tallafawa Talakawa – Sarkin Saminaka

Mai martaba Sarkin Saminaka da ke jihar Kaduna, Alhaji Musa Muhammad Sani, ya yi kira ga Gwamnatocin kasar nan, da su fitar da kayan abincin…

Mai martaba Sarkin Saminaka da ke jihar Kaduna, Alhaji Musa Muhammad Sani, ya yi kira ga Gwamnatocin kasar nan, da su fitar da kayan abincin da suka ajiye su rabawa talakawa domin rage radadin mawuyacin halin da suke fama da shi, na rashin abinci.

Sarkin ya yi wannan kira ne, a lokacin da ya ke jawabi a wajen taron bikin Maulidi, da aka gudanar a garin Saminaka a ranar Alhamis.

Sarkin ya yi bayanin cewa daukar wannan mataki, ya zama wajibi ganin irin abin da ya faru a yan kwanakin nan, inda talakawa suka rika fasa wuraren da aka ajiye abinci a kasar nan.

Ya yaba wa al’ummar yankin Saminaka, kan yadda basu shiga wannan al’amari na fashe-fashen wuraren da aka ajiye, abinci ba.

Ya yi kira ga shugabannin addini, su cigaba da yin addu’o’i, domin  addu’a ce kadai magannin dukkan matsalolin da suke damun mu, a kasar nan.