Gwamnati ta haramta shigo da tumaturin gwangwani qasar nan | Aminiya

Gwamnati ta haramta shigo da tumaturin gwangwani qasar nan

 

A kwanakin baya ne Gwamnatin   Tarayya   ta haramta shigowa da tumaturin gwangwani daga kasashen waje zuwa cikin kasar nan ta kan iyakokin kan kasa. Wannan mataki ya biyo bayan koke-koken da kamfanonin sarrafa tumaturin gwangwani suka rika yi a lokuta da dama ne kan irin kalubalen da suke fuskanta wajen tafiyar da kamfanoninsu. Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba  Jari, Dakta  Okechukwu  Enalamah ne  ya  sanar  wa  manema  labarai  hakan, jim kaxan bayan fitowarsa daga zaman Majalisar Zartarwa a ranar Larabar makon jiya.

Ministan   ya  ce  Majalisar   Zartarwa a karkashin jagorancin Mukaddashin Shugaban  Kasa,  Farfesa  Yemi  Osinbajo ta amince da hakan ne tare da kafa wani kwamiti wanda zai duba tsarin masana’antu da cinikayya  da zuba jari da kuma gasa a tsakanin kamfanoni don daidaita farashi, musamman  a wannan  lokaci da kasar ke kokarin farfaxowa daga tabarbarewar tattalin arziki.

Ministan tare da rakiyar Ministar a Ma’aikatar  Masana’antu,  Kasuwanci  da Zuba Jari, Hajiya A’isha Abubakar, ya ce Gwamnatin Tarayya ta xauki wannan mataki ne a kokarinta na inganta harkokin kasuwanci tare da jawo hankalin masu zuba jari a cikin kasar nan. Kuma ya ce wannan zai rage yawan asarar da manoman tumatir ke yi, wadda kwararru suka kiyasta ta kai kashi 40 cikin 100 na tumatir xin saboda rashin kyakkyawan yanayin ajiyarsu.

“Koda yake haramci ya shafi shigowa da tumaturin gwangwanin ne ta kan iyakokin kasa, amma an amince a rika shigowa da su ta hanyar ruwa kawai. Kuma ta ruwan ma ba a amince da shigowa da tumaturin a sarrafe cikin gwangwani ba, sai dai a shigo da shi kana a sarrafa cikin gwamgwanin a nan Najeriya, kuma Najeriya ta kyale shigowa da tumatir xin ne ta ruwa don girmama kudirin Kungiyar Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS),” inji shi.

“Don   haka   mun   amince   cewa   duk wanda aka kama da karya wannan doka, to babu shakka zai biya kashi 50 cikin 100 na adadin kuxin abin da ya sayo, don karya kwarin gwiwar masu shigowa da su cikin Najeriya  ta yadda  nan gaba  kowa  zai ga alfanun amfani da ababen da kasarmu ke nomawa,” inji shi.

Bugu da kari Ministan ya tabbatar da cewa Najeriya za ta kara inganta harkokin masana’antunta nan ba da jimawa ba, ta yadda ’yan Najeriya za su rika wadatuwa da albarkatun kasarsu kamar sauran kasashen da suka ci gaba a duniya. Ya ce Najeriya na shigo da tumatirin  gwangwani  da ya kai tan dubu 150, wadda ya kai kimanin Dala miliyan 170 a shekara.

“Haka kuma wannan tsari zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga ’yan Najeriya dubu  60 ta hanyar  masana’antun sarrafa tumaturi a Najeriya sannan tumaturin zai wadata cikin kasa da kimanin tan miliyan biyu  da rabi,” inji shi.

Yawa-yawan ’yan kasuwa da masu sarrafa tumaturin gwangwani sun yaba da wannan  mataki  da  Gwamnatin  Tarayya ta xauka na hana shigowa da tumaturin gwangwanin zuwa Nijeriya daga kasashen waje.

Haka  zalika  baya  ga  hani  kan  shigo da tumaturin gwangwanin, gwamnati ta kuma kara kuxin haraji a kan tumaturin da ake shigowa da shi daga ketare koda ba a riga an sarrafa shi ba.

Gwamnati  ta ce ta xauki  matakan  ne da zimmar karfafa manoman tumatir na cikin  gida  tare  da taimaka  wa  waxanda suke sarrafa timaturin a cikin gida.

Matakin da gwamnati  ta xauka dai ya biyo bayan koke-koken da masu sarrafa tumaturin  gwangwanin  suka rika yi bisa yadda tumaturin gwangwanin kasashen ketare ke karya musu tasu kasuwar,  haka kuma a cewarsu na cikin gidan ya fi inganci nesa  ba kusa  ba, inda  wannan  korafi  ya yi matukar tasirin da ya kai su ga yin barazanar rufe masana’atunsu baki xaya.

Shugaban Kamfanin Tumaturin Gwangwani mafi girma a Afirka da ke Legas, Cif Eric Nwofia ya bayyana jin daxinsa  game  da  wannan  mataki,  inda ya  ce  Allah  ne  Ya  amshi  addu’arsu   Ya biya musu wannan bukata da suka jima suna   jiran   zuwanta.   Ya  kara   da  cewa kukan da suka jima suna yi ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ji, saboda Shugaba ne mai son gaskiya da kuma aiki da ita a kowane lokaci.

Alkalumma  sun  nuna  cewa  Najeriya na  kashe   kimanin   Naira   biliyan   52  a kowace shekara wajen shigo da tumaturin gwangwani kimanin tan dubu 150 zuwa cikin kasar nan. Lamarin da yake haifar da tarnaki tare da hana bunkasar kamfanonin cikin gida da su kansu manoman.

Su ma manoman tumatir a sassar kasar nan, sun nuna jin daxinsu kan wannan mataki da Gwamantin  Tarayya  ta xauka, inda suka kwatanta da hanin shigo da shinkafa zuwa Najeriya, wanda ya taimaka wa manomanta.