✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta haramta wa baburan A Daidaita Sahu bin manyan titunan Kano

Hukumar ta ce akwai yiwuwar a sake hana wasu bin wasu titunan a nan gaba

Gwamnatin jihar Kano ta haramta wa matuta babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidaita Sahu bin wasu manyan titunan jihar daga ranar Laraba ma zuwa.

Haramcin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar (KAROTA) ta fitar da sanyin safiyar Talata, ta bakin Kakakinta, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa.

A cewar sanarwar, “Gwamnatin ta dauki matakin ne bayan da ta samar da manyan motocin da za su dinga daukar al’umma a titunan da aka haramta wa ’yan Adaidaita Sahun bi.”

Sanarwar ta kuma ce an titunan da aka haramta wa baburan bi sun hada da Ahmadu Bello da titin Mundubawa Zuwa Gezawa (Hadeja Road) da kuma titin Tal’udu zuwa Gwarzo.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta tanadi manyan motocin sufuri domin saukaka wa al’umma bin wadannan hanyoyi.

Kazalika, KAROTA ta kara da cewa za ta sanar da ranar da matuka Adaidaita Sahun za su daina bin wasu manyan titinan da zarar gwamnatin ta samar da ababen hawan da al’umma za su yi amfani da su a wadannan hanyoyi.

Sai dai, hukumar ta ce akwai yiwuwar a sake hana bin wasu titunan a nan gaba da zarar an samar da wadatattun motocin da za su rika bin titunan.

Galibi dai harkar sufuri a birnin Kano ta ta’allaka ne ga baburan na Adaidaita Sahu, inda kusan a yanzu za a iya cewa sun kori galibin motocin bas-bas da na Tasi daga birnin, wadanda a yanzu suka koma zuwa wasu garuruwan na ciki da wajen jihar.