✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta kafa kwamitin shawo kan tsadar kayan masarufi

Kayan masarufi sun tashin gwauron-zabo a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi zaman gaggawa don warware matsalar tsadar kayan masarufi a fadin Najeriya.

Zainab Ahmed, Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare ce ta bayyana haka a ranar Laraba, jim kadan bayan fitowa daga taron Majalisar Zartarwart ta Kasa, wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Ta ce kwamitin ya ba da umarnin shawo kan matsalar tashin kayan masarufi cikin gaggawa, inda ta ce tuni aka nemo wasu hanyoyi da za su rage tashin da kayan masarufin suke yi.

Ministar ta ce an yi wa kwamitin bayani yadda abubuwa suka yi tashin gwauron-zabo da kuma yadda za a kawo karshen matsalar.

Tsadar kayan masarufi dai matsala ce da ke ci wa talakawa tuwo a kwarya, wanda mutane da dama suka dinga kiraye-kiraye ga Gwamnatin Tarayya da ta yi wani abu don magance ta.

Kayan abinci da sauran kayan al’amuran yau da kullum sun yi tsadar da mai karamin karfi ba zai iya sayensu din ya yi tanadi ba.

Hakan ta jawo ta’azzarar abubuwa da dama, wanda mutane da yawa yanzu abinci ke neman gagararsu.