✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta kwace filin ginin da ya rushe a Kano

Gwamnati za ta mayar da wajen filin ajiye ababen hawa

Gwamnatin Jihar Kano ta soke izinin mallakar filin da bene mai hawa uku ya rushe a kasuwar wayoyin hannu ta Beirut Road da ke Kano.

Ginin dai, wanda ya rushe a ranar Talata, ya yi sanadin rasuwar mutum biyu, yayin da wasu bakwai suka jikkata.

Kodayake ba a bayyana wanda ya mallake shi ba, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ta ce tun da farko ba a gina shi bisa ka’ida ba.

Sai dai a yayin wata ziyara da ya kai wajen ranar Laraba, Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya ce yanzu za a mayar da filin wajen ajiye ababen hawa.

A cewarsa, “Tun farko ma nan wajen kamata ya yi a mayar da shi wajen ajiye ababen hawa. Ya yi kankanta a gina shaguna.”

Ganduje ya kuma ce an kafa wani kwamiti mai karfi da zai binciki musabbabin rushewar ginin.

Ya ce, “Ya kamata mu san cewa tun da farko, ya kamata kwararru su zana tare da sanya ido a kan aikin ginin wajen. Wannan kwamitin da kuka kafa zai yi aikinsa cikin mako daya sannan ya mika mana rahotonsa.”

Daga nan sai Gwamnan ya roki ’yan kasuwar da ke wajen da su ba masu aikin kwashe baraguzan ginin hadin kai, inda ya ce da zarar sun kammala za a mayar da shi wajen ajiye ababen hawan.