✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta rufe gidan rediyon Brekete

Hukumar NBC ta dakatar da lasisin gidan rediyon Brekete.

Gwamnatin Tarayya ta rufe gidan rediyon Brekete, bayan da Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin (NBC) ta dakatar da lasisinsa.

NBC ta sanar da dakatar da lasisin gidan rediyon ne a ranar Alhamis, bayan wani kai-komo da mai shi kan zargin cin mutunci.

A kwanakin baya ne aka fara kullin kurciya bayan wani rahoto da ya nuna bidiyon mai gidan rediyon kuma mai gabatar da shirin ‘Brekete Family’, Ahmed Isah yana bugun wata bakuwar shirin.

Daga baya, ya bayar da hakuri a cikin shirin ga matar game da abin da ya faru da kuma yadda ya wuce makadi da rawa wajen hawa dokin zuciya.

Sanarwar da NBC ta fitar ta ce ta karbi uzurin da dan jaridar ya gabatar da kuma nadamar da ya nuna, amma da sauran rina a kaba.

Ta ce, “Abin da mai gabatar da shirin ya yi ya saba Kundin Gabatar da Shirye-shirye, ha’inci ne kuma ga amanar da mutane da gwamnatin Najeriya suka ba shi, wadanda kuma a madadinsu aka ba da lasisin gidan rediyon, bisa yarda.

“Sashe na 0.1.1.2.1 na Kundin ya bayyana cewa manufar yada shirye-shirye ga al’umma ita ce – ‘yada dabi’u da al’adu nagari musamman sanin ya kamata da mutunci da girmamawa ga  dan Adam’.