✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: An rufe layukan sadarwa a Zamfara

NCC ta ba da umarnin rufe ayyukan kamfanonin sadarwa gaba daya.

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta ba da umarnin rufe layukan sadarwan daukacin kamfanonin waya a Jihar Zamfara.

Umarnin rufe layukan sadarwan ya fara aiki ne ranar Juma’a a wani mataki na ba wa hukumomin tsaro damar gudanar da aikinsu a Jihar Zamfara, wadda matsalar ayyukan ’yan bindiga ta yi kamari.

Sanarwar da NCC ta fitar ta ce, “Ci gaban matsalar tsaro a Jihar Zamfara ya sa dole a rufe layukan sadarwa gaba daya a fadin jihar daga yau Juma’a, 3 ga Satumba, 2021.

“Hakan zai ba wa hukumomin tsaron da suka dace damar yin abin da ya kamata na dawo da tsaro a jihar.

“Saboda haka ake umartar Globacom ya gaggauta rufe duk tashoshin sadarwa da suke a fadin jihar da ma wadanda ke jihohi masu makwabtaka da ita da za a iya amfani da su wurin sadarwa a cikin jihar.”

Sanarwar ta kara da cewa za a rufe layukan sadarwan ne na tsawon mako biyu a karon farko.

Umarnin rufe layukan sadarwa a Jihar Zamfara na zuwa ne kwana biyu bayan ’yan bindiga sun kai hari a wata makarantar sakandare da ke kauyen Kaya a Karamar Hukumar Maradun ta jihar, suka yi awon gaba da dalibai maza da mata sama da 70.

Harin makarantar ya sa Gwamnatin Jihar Zamfara rufe makarantu a fadin jihar, sai abin da hali ya yi.

An kai wa makarantar harin na ranar Laraba ne washegarin da gwamnatin jihar da wasu makwabtanta suka fara rufe wasu manyan hanyoyi da kasuwannin dabbobi da sauran matakai a wani yunkuri na fatattakar ’yan bindiga.

Matsalar hare-haren ’yan bindiga ta lakume dubban rayuka baya ga asarar duniyoyi masu yawa, da kuma raba al’ummomi da muhallansu.