✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta sa a binciki hatsarin jirgin kasa a Legas

Mutum shida sun mutu wasu 79 sun jikkata a hatsarin jirgin kasa da motar ma'aikata

Ministan Sufurin Jirgin Sama, Sanata Hadi Sirika, ya bai Hukumar Binciken Tsaro (NSIB) umarni gaggauta bincike game da hatsarin da ya auku tsakanin jirgin kasa da wata motar daukar ma’aikata ranar Alhamis a Legas.

Sirika ya bayyana hatsarin, wanda ya ya yi ajalin mutum shida da jikkatar wasu 79, a matsayin abin tashin hankali, tare da bai wa al’umma tabbacin hukumar NSIB za ta binciko musabbabinsa don kiyaye aukuwar hakan a gaba.

Cikin sanarwar da ya fitar ta bakin hadiminsa, Dokta James Odaudu, ministan ya bukaci hadin kan al’umma don cimma nasarar binciken da za a gudanar.

Daga nan, Sirika ya jajanta wa gwamnati da ma al’ummar Jihar Legas dangane da hatsarin, musamman ga wadanda suka rasa ’yan uwansu a iftila’in.

Rahotanni daga yankin sun ce mutum uku sun riga mu gidan gaskiya, sannan da dama sun jikkata sakamakon hatsarin.