Gwamnati ta samar wa ’yan sanda kayan aiki | Aminiya

Gwamnati ta samar wa ’yan sanda kayan aiki

Salam Edita, ka ba ni dama in yi kira ga Gwamnatin Tarayya kan ta samar wa ’yan sanda sababbin kayan aiki na zamani da motocin aiki, lura da yadda sacewa da garkuwa da mutane suka zama ruwan dare a kasarmu. Akwai bukatar gwamnati ta samar wa ’yan sanda sababbi kuma ingantattu kayan aiki na zamani da motoci masu shiga daji da yashi da tabo domin dakile harin ’yan ta’adda da garkuwa da mutane, kasancewa kayan da suke amfani da su yanzu tsofaffi ne marasa inganci.

Daga Jibril Abba Ocal, Birnin Kebbi. 08053952787.