✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta san za a kai Harin Kuje, ta ki yin komai —Tukur Mamu

Mai shiga tsakani ya ce hukumomin gwamnati sun samu rahoto yiwuwar harin, amma ba su dauki matakin da ya dace

Mai shiga tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar Ansaru domin ganin an sako fasinjojin jingin kasan Abuja-Kaduna, Tukur Mamu, ya ce gwamnati ta samu rahoton yiwuwar kai harin Kurkukun Kuje, amma ta ki daukar matakan dakile shi.

Tukur ya ce kungiyar Ansaru ce ta kai harin, wanda a sanadiyyarsa, daukacin mayakan Boko Haram da suke tsare a gidan yarin suka tsere.

“Zan iya tabbatar muku cewa kungiyar da ta kai wa jirgin kasan Abuja-Kaduna hari ce ta tsara ta kuma aiwatar da Harin Gidan Yarin Kuje, saboda sun nuna take-taken hakan, wanda na riga na sanar,” inji shi a ranar Laraba, yana mai nuna damuwa kan rashin daukar matakan dakile barazanar daga bangaren gwamnati.

Ya ci gaba da cewa, “A sani cewa sun nemi a saki mambobinsu guda 51, amma da muka yi ta ttauunawa, ni kadai na samu suka rage zuwa mutum 10, na kuma sanar da hukumomin da suka dace, na ba su sautin da na nada a matsayin hujja.

“Sai dai kuma gwamnati ta yi ta jan kafa, ta kasa ba su amsa.

“Ga shi yanzu sun yi nasarar kai wani hari da ya nuna gazawar tsarinmu na tattara bayanan sirri wajen daukar matakan dakile barazana a kan kari.

“Sun kuna kubutar da mambobinsu, wanda za a iya kawarwa ta hanyar amincewa da bukatarsu a ba su mutum 10 su sako fasinjojin da ke hannunsu.

“Duk wadannan tattaunawa da na sayar da raina na yi, duk da cewa gwamnati ta ki fitowa ta tabbatar, ina da hujjoji na sauti sama da 100 da na nada na kuma ba wa hukumomin da suka dace.

“Saboda muhimmancin wannan sanarwar ’yan jarida kuma, na fitar da wasu sabbin muryoyi da na nada guda gudu,” in ji Tukur Mamu.

ISWAP ta yi ikirarin harin

Sai dai kuma a wani sabon bidiyo da kungiyar ISWAP mai biyayya a IS ta fitar, ta yi ikirarin kai harin na Kuje.

A sakon da ISWAP ta fitar tare da bidiyon harin ta shafinta a ranar Laraba, ta ce, “Mayakan Daular Musulunci sun yi nasarar kai hari a Gidan Yarin Kuje da ke wajen garin Abuja a jiya (Talata) inda suka rusa katangar wurin suka kubutar da gomman fursunoni.”

Bidiyon na ISWAP ya nuna irin luguden wuta da kone-kone da maharan suka yi a cikin harabar gidan yarin.

An kuma ji suna kabbara suna cewa, “Daular Musulunci ba za gushe ba.”

Masu bibiyar ayyukan ta’addancin kungiyoyi masu ikirarin Jihadi sun bayyana cewa Ansaru wani bangare ne da ya balle daga kungiyar Boko Haram saboda adawa da wasu tsare-tsaren Boko Haram.

Ita ma ISAWP wani bangare ne na Boko Haram da ya balle, amma dukkansu na da alaka da kungiyar IS.