✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta sauya wa Kwalejin Afaka matsugunni

A watan Maris ne ’yan bindiga suka kai hari Kwalejin, inda suka sace dalibai mata zalla.

Gwamnatin Tarayya ta sanar da kammala shirinta na sauya matsugunin Kwalejin Horar da Harkokin Noma da Gandun Daji ta Afaka da ke Jihar Kaduna.

Hakan na zuwa ne bayan sace dalibai 37 da ’yan bindiga suka yi tare da tsare su na tsawon kimanin watanni biyu gabanin sakinsu.

Sai dai gwamnatin tarayya ba ta fayyace matsugunin da ta maida makarantar ba kamar yadda Shugabanta, Mista Usman M. Bello ya bayyana.

Yayin ganawa da manema labarai da Ma’aikatar Muhallin Jihar Kaduna ta yi, Bello ya ce gwamnati ta gama shirye-shiryen sauya wa kwalejin wuri na wucin-gadi domin tabbatar da ingantaccen tsaro.

Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta samar da motocin da za su kwashe malamai da dalibai har da kayyakinsu daga garin Afaka zuwa sabon wurin da aka sauya wa Kwalejin.

A kan haka yake rokon iyayen dalibai da su ba su damar komawa sabon wurin da aka maida Kwalejin don kammala karatunsu, inda ya bayar da tabbaci cewa an tanadi wuraren kwana da na karatu masu inganci ga daliban.

A cewarsa, “Ministan Mahalli ya ba da umarnin a yafe wa daliban da aka sace kudin makarantar na wannan zango.

“Sannan ya sake ba da umarnin yafe kudin makarantar ga daliban da suke yin karatun Difloma ta (ND),” a cewar Bello.

Kazalika, Bello ya yi karin haske da cewar tsohon ginin Kwalejin za a maida shi cibiyar nazari da bincike na wucin gadi har zuwa lokacin da sha’anin tsaro zai inganta a jihar.

Wasu daga cikin iyayen daliban Kwalejin sun bayyana farin cikinsu kan matakin da gwamnatin ta dauka na amincewa da bukatar sauya wa kwalejin matsugunni.

Friday Sanni, wanda ’ya’yansa biyu mata na daga cikin wadanda ’yan bindigar suka sace, ya ce wannan hukunci zai ba wa iyaye da dama kwarin gwiwar dawo da ’ya’yansu makarantar.

Ana iya tuna cewa, a watan Maris ne wasu gungun ’yan bindiga suka kai hari Kwalejin Horas da Harkokin Noma ta Gwamnatin Tarayya wato Federal College of Forestry Mechanisation, inda suka sace dalibai mata zalla.