✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta umarci kafafen yada labaran Najeriya su rufe shafukansu na Twitter

An umarci dukkan kafafen yada labarai da su rufe shafukansu na Twitter nan take.

Hukumar Kula da Harkokin Yada Labarai a Najeiya (NBC), ta umarci dukkan kafafen yada labarai da su rufe shafukansu na Twitter nan take.

Wannan umarni na dauke cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Hukumar, Farfesa Armstrong ya fitar a safiyar ranar Litinin.

“Biyo bayan umarnin dakatar da ayyukan shafin Twitter da Gwamnatin Tarayya ta yi saboda yadda dandalin ke ba da gudunmuwar rushe hadin kan kasar nan, Hukumar Kula da Harkokin Yada Labarai ta Kasar tana umartar dukkanin tashoshin watsa labarai a Najeriya da su rufe tare da daina amfani da shafukansu na Twitter nan take.

“Sashe na 2(1) na dokar NBC ya gindaya cewa Hukumar na da hakkin tilasta bin dokokin kasa tare da mutunta dukkan tsare-tsarenta.

“Sannan sashe na 3.11.2 ya tanadi NBC ta tilasta aiwatar da doka a kowane lamari da bukatar hakan ta taso domin tabbatar da cewa an kiyaye doka da oda wanda muhimmancin hakan ya zarta aikata laifi da rashin tsari mai cike da hatsaniya,” a cewar sanarwar.

Kazaliika, ya janyo hankalun masu watsa labaran zuwa sashi na 5.6.3 na dokar wanda ya yi tanadin a lura da ababen da ka iya janyo kiyayya ko haifar da tarzomo a tsakanin al’umma.

Ya ce akwai rashin kishin kasa ga duk wasu masu watsa labarai a Najeriya da suka ci gaba da amfani ko tallata shafin Twitter da aka dakatar a matsayin mabubbugar samun labaransu.