✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnati ta umarci masu ajiya a banki su sabunta rajistarsu

Za a rufe asusun ajiyar wadanda ba su sabunta rajista ba ko kuma a ci su tara

Gwamnatin Tarayya ta umarci duk mai ajiya a bankunan Najeriya ya sabunta rajista shi.

Sanarawar da ta fitar kan hakan a ranar Alhamis ta ce gwamnatin za ta dauki mataki kan wadanda suka ki sabunta rajistarsa ba.

“Za a kuma dauki matakin duk wanda bai cika fom din ba cire kudi daga asusunsa ko kuma cin sa tara”.

Sanarwar ta ce, “Ana kira ga masu ajiya a wuraren hada-hadar kudi (Bankuna da kamfanonin ishora) su karbi fom, su cika shi, sa’annan su mayar bankunansu.

“Wadanda kuma ke da asusun ajiya a bankuna daban-daban za su cika fom din su kai kowanne daga cikin bankunan.

“A kwai bukatar a tsara fomafoman da wuraren hada-hadar kudin za su raba su bi tsarin dokar harajin kudi na 2019.

“Fom din da kowa zai cika yana da bangarori 3: Fom din kamfani – (na masu jari da amintattu da sauransu – Fom din mutum daya”, inji sanarwar.

Umarnin na zuwa ne duk da mallakar lambar shaida ta BVN da kowane mai asusun ajiya ya mallaka a kasar.