✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta yi wa daliban da ke karatu a Ukraine tayin guraben karatu a jami’o’in Najeriya

Tayin na zuwa ne lokacin da ASUU ta shiga wata na 5 tana yajin aiki

Gwamnatin Najeriya ta yi wa daliban Najeriya da ke karatu a kasar Ukraine kafin mamayar Rasha tayin ba su guraben karatu a jami’o’in  Najeriya duk da yajin aikin da malaman jami’o’i ke ci gaba da yi a kasar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ce ta sanar da shirye-shiryenta na mayar da daliban da ke karatu a kasar ta Ukraine a cikin wata sanarwa.

Ma’aikatar ta ce tuni shirye-shirye suka yi nisa don ganin an sama wa wadannan dalibai guraben karatu a jami’o’in gwamnati.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da  mai magana da yawun Ma’aikatar, Francisca K. Omayuli, ta sanyawa hannu a ranar Litinin, hudu ga Yulin 2022.

Sanarwar ta ce dalibai masu sha’awar  ci gaba da karatun a gida su hanzarta ziyartar shafin ma’aikatar domin cike bayanansu ta intanet kafin ranar 15 ga watan Yulin da muke ciki.

A halin yanzu, kimanin watanni biyar ke nan Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta tsuduma yajin aiki wanda har yanzu ba a san ranar dawowarta ba.

Tun bayan da Rasha ta kaddamar da yaki a kasar Ukraine dai, miliyoyin mutane, ciki har da daliban Najeriya da ke karatu a can, suka bar kasar bayan sun yi gudun hijira.

Tun lokacin ne dai karatun nasu ya sami tsaiko, kuma ba su san ranar komawar su ba don ci gaba da karatun.