✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Gwamnati Tarayya ta dora alhakin karuwar talauci a kan gwamnoni

Gwamnatin tarayya ta ce gwamnoni ba su damu da ayyukan da za su ciyar da al'umma gaba ba.

Gwamnatin Tarayya ta dora alhakin karuwar talauci a tsakanin al’umma a kan gwamnonin jihohin kasar.

Karamin Ministan Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare, Clem Agba ne ya shaida wa manema labarai hakan bayan Taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya a ranar Laraba.

A cewar Ministan, Shirin Zuba Jari da Gwamnatin Tarayya ta assasa bai yi tasiri sosai ba, saboda rashin hadin kai da aka samu daga bangaren gwamnonin jihohi.

Mista Agba ya kara da cewa gwamnonin sun maida hankali ne wajen aiwatar da ayyukan bogi, maimakon inganta rayuwa al’umma musamman mazauna yankunan karkara.

Ministan ya kuma ya bayyana takaicinsa kan yadda gwamnonin suka mayar da hankali wajen aiwatar da manya-manyan ayyuka kamar ginin gadar sama, filayen jiragen sama da dai sauransu da ake iya gani a manyan biranen jihohi, maimakon gina hanyoyin da za su dakile wa manoma asarar amfanin gona bayan sun yi girbi.

Ministan ya yi nuni da cewa, a yayin da jihohi ke kula da filayen noma, ba sa saka hannun jari a cikinsu domin amfanin al’ummarsu na karkara.

Don haka ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina yi wa gwamnonin rikon sakainar kashi yayin da ya shawarci gwamnonin da su mayar da hankali kan ayyukan da za su iya fitar da jama’a daga kangin talauci.

An iya tuna cewa, a sakamakon mamakom ruwan sama sa aka samu a daminar bana a fadin Najeriya, jihohi da dama musamman na Arewacin Najeriya sun fuskanci mummunar ambaliyar ruwa, lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dukiya mai dimbin yawa.