✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati za ta ba da kwangilar tsaron Jirgin Kasan Abuja-Kaduna

Gwamnati na duba yiwuwar bai wa kamfanoni masu zaman kansu aikin samar da tsaro a bangaren sufurin jiragen kasa

Gwamnatin Tarayya tana duba yiwuwar mika wa kamfanoni masu zaman kansa aikin samar da tsaro ga layin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Ministan Sufuri, Muazu Sambo, ya ce hakan na daga cikin matakan da gwamnati take tunanin dauka a shirinta na daukar ingantattun matakan tsaro ga sufurin jirgin kasa.

Ministan ya ce, “Muna duba yiwuwar hadin gwiwa da ’yan kasuwa, domin akwai wasu kwararrun kamfanoni tsaro da suka magance irin wannan matsalar a wasu kasashe.

“Muna tunanin ba su kwangilar aikin sannan muna nazarin irin kudaden da za a kashe da sauran abubuwa domin hakarmu ta cimma ruwa.”

Da yake jawabi bayan tsaron Majalisar Zartarwa ta Kasa, ministan ya ce, “Akwai wata fasaha da Gwamnatin Jihar Kano take amfani da ita a Dajin Falgore da amincewar Hukumar DSS.

“Muna duba yiwuwar amfani da ita da kuma kudin da zai ci; Misali idan tsaron layin jirgin Abuja-Kaduna ya ci N3bn zuwa N9bn, to nawa za ta kashe ke nan a fadin Najeriya?”

Sai dai ya bayyana cewa amfani da na’urar wadda za ta samar da tsaro ta hanyar amfani da fasahar hangen nesa za ta taimaka wajen samar da tsaro a kan layin jirgin kasan.

“Duk fasahar da muka yi amfani da ita a Abuja-Kaduna, idan har ya yi nasara, to shi za a dabbaka wajen samar da tsaro daukacin layin jirgin kasa da ke Najeriya,” inji ministan.

A kasafin shekarar 2o22 dai gwamnatin ta ware Naria biliyan 71.67 domin sanya na’urar sanya ido na zamani a layin jirgin da ke tsakanin Abuja da Kaduna.

Ministan ya bayyana cewa majalisar ta amince da Naira biliyan 1.49 domin gyaran janwai din jirgin kasan.

Wauta ne dawo da jirgin kasan Kaduna-Abuja

Game da dawowar aikin jirgin kasan Abuja-Kaduna kuwa, ministan ya ce yin hakan a yanzu tamkar rashin damuwa da iyalai da kuma fasinjojin jirgin da ’yan ta’adda suka sace ne.

Ya bayyana cewa gwamnati tana aiki ka’in-da-na’in domin samo fasahar da za ta tabbatar da samun ingantaccen tsaro a bangaren sufurin jiragen kasa domin kauce wa maimaituwar abin daya faru da jirgin kasan Abuja-Kaduna.