✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati za ta kara kudaden haraji a 2022 —Ministar Kudi

Za a kara kudaden harajin da ake karba daga daidaikun mutane da kamfanoni

Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, ta ce akwai yiwuwar Gwamnatin Tarayya ta kara kudaden harajin da take karba daga shekarar 2022 mai kamawa.

Ministar ta bayyana cewa akwai yiwuwar kara kason da ake karba na kudaden haraji daga daidaikun mutane da kamfanoni a 2022 saboda halin matsin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki.

“Daftarin dokar kudi ya yi tanadin sauyi a hajarin kudaden shigar mutane, harajin yin sayayya (VAT), harajin kan sarki, dokar harajin ribar kamfanoni, dokar kudaden shikgar kamfanoni, dokar kafa hukumar FIRS da sauransu,” inji ta.

Ta sanar da haka ne a ranar Litinin a jawabinta ga masu ruwa da tsaki a lokacin taron sauraron ra’ayoyin jama’a kan Kudurin Dokar Kudi da Majalisar Wakilai ta shirya a Abuja.

Ministar ta bayyana cewa akwai sauye-sauye da dama da kudurin dokar kudi ya tanada, wadanda za su fara aiki a tsakiyar shekara mai zuwa.

Ta ce sauye-sauye sun shafi bangaren kudade kuma ma’aikatarta ta karbi shawarwari a kansu daga wurin masu ruwa da tsaki.