✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati za ta kashe N999m kullum don ciyar da ’yan makaranta 10m

Za a rika kashe N100 kullum ga yara miliyan 10

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta rika kashe Naira miliyan 999 a kullum a shirinta na ciyar da yara ’yan makaranta kimanin miliyan 10 a Najeriya.

Hajiya Aishatu Digil, jagorar shirin ce ta bayyana hakan a Abuja ranar Talata, yayin taron masu ruwa da tsaki a shirin kan hanyoyin da za a bi wajen aiwatar da shi.

Ta ce tuni Ministar Jinkai da Walwalar Jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouk ta sami sahalewar kashe N100 kan ciyar da kowane yaro dan makaranta a kullum.

Ta ce za a fara ciyar da ’yan aji daya zuwa uku na firamare su kimanin 9,990,862 da abincin N100 a kullum, wanda kudin za su kama N999,086,200.

“Kafin wannan yunkurin, mukan ciyar da yaran ne da N70 a kullum tun shekarar 2016, amma yanzu Shugaban Kasa ya ba da umarnin kara farashin zuwa N1000.

“Muna kiran dukkan masu ruwa da tsaki kamar Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Kididdiga ta Kasa da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) da Ma’aikatar Noma da ta Ilimi da su tattauna hanyoyin rarraba kudaden.

“Muna taron nan ne don mu ga yadda za mu aiwatar da shirin a kan sabon farashin don a inganta abincin da ake ba daliban.

“Yadda za a kasafta N100 shi ne kamar haka; N70 kudin dukkan kayan hadi ban da kwai, sai N14 kudin kwai da za a rika sayen shi tare da tallafin Kungiyar Masu Kiwon Kaji ta Najeriya.

“Muna shirin samar da ‘Larabar Kwai’, inda kowane daga cikin daliban za a rika ba shi kwai a duk ranar Laraba.

“N10 kudin masu girki ce, N11 kuma kudin sinadaran girki sai kuma Naira daya ta masu duba ingancin abincin, amma ba dole ba ce,” inji ta.