✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati za ta yi kidayar jama’a a Sambisa

'Matsalar tsaro ba za ta hana ni aiwatar da shirin kidaya a Sambisa ba'

Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), Nasir Kwarra, ya ce matsalar tsaro ba za ta hana shi gudanar da aikin na bana a Dajin Sambisa ba.

Saboda a cewarsa, wajibi ne su ma mazauna yankin a kidaya.

Ya ce, an riga an kididdige gidaje a dajin a lokacin da aka gudanar da shirin tantance gidaje, don haka babu abin da zai hana shi gudanar da kidayar a wasu sassan kasar.

Kwarra ya bayyana haka ne a wajen taron auna ayyukan gwamnatin Buhari karo 24 ranar Alhamis a Abuja.

Ya kara da cewa, kawo yanzu kudi sama da N100bn aka kashe wajen shirye-shiryen kidayar ta bana.

Da yake jawabi, Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya ce shirin kidaya na wannan karon zai kafa sabon tarihi a Najeriya saboda kyakkyawan shirin da gwamnati ta yi.