✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Adamawa za ta kashe N821m don gyaran titi da sanya fitilun hanya

Gwamnatin Adamawa ta amince da fitar da Naira miliyan 821 domin sabunta titunan birane da sanya fitilun kan hanya a kananan hkumomin jihar uku. Kwamisinan…

Gwamnatin Adamawa ta amince da fitar da Naira miliyan 821 domin sabunta titunan birane da sanya fitilun kan hanya a kananan hkumomin jihar uku.

Kwamisinan yada labarai na jihar Umar Pela ne  ya bayyana wa Aminiya ranar Laraba cewa hakan ya biyo bayan matakin majalisar zartaswar jihar, na hanzarta aiwatar da shirin sabunta birane da Gwamna Ahmadu Fintiri ya fara.

Ya ce tuni ka fitar da wasu Naira miliyan 329, domin samar da titi mai nisan kilomita daya daga Jada zuwa Mbulo.

“An yanke shawarar kara tsawon titin ne, yayin ziyarar da gwamnan ya kai garin Jadan a baya-bayan nan,” in ji shi.

Kwamishinan ya ce majalisar zartaswar ta kuma amince da fitar da Naira miliyan 492 don sanya fitilu masu amfani da hasken rana, a titin Atiku Abubakar da ke Jimeta, da Yola ta Kudu, da kuma titin Mubi da ke karamar hukumar Mubi.

“Za a kashe kusan Naira miliyan 492 a ayyukan, kuma ana sa ran kammalawa cikin watanni uku,” in ji shi.