✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Borno za ta kwace kadarorin Majalisar Dinkin Duniya

Gwamnatin Borno ta ba wa hukumomin Majalisar Dinkin Duniya wa'adain kwana 30 za ta kwace kadarorinsu saboda kin biyan haraji.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya ba wa hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ke jihar wa’adain kwana 30 zai kwace kadarorinsu saboda kin biyan haraji.

A ranar Laraba ce Gwamnatin Jihar Borno ta sanar cewa za ta fara kwace kadarorin wasu hukumomi bakwai na Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a jihar, saboda rashin biyan haraji.

Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Jihar Borno (BO-IRS), Mohammed Alkali, ya ce, “Tun a watan Janairun 2021 muke kokarin ganin hukumomin sun biya kudaden harajin, amma suka ki, saboda haka BO-IRS ta ba su wa’adin kwana 30 zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu, 2022, za ta kwace kadarorinsu.

“Sanarwar da aka ba su za ta halasta wa hukumar amfani da karfinta wajen kwace kadarorin hukumomin da abin ya shafa,” inji shi.

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya bakwai da gwamnatin Bornon za ta kwace wa kadarori su ne: Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Shirin Samar da Abinci na Duniya (WFP), da kuma Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR).

Sauran su ne Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), Ofishin Bayar da Agaji na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA), Hukumar Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO), da kuma Shirin Cigaba na Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) da suke da ofisoshi a Maiduguri.

Mohammed Alkali ya bayyana cewa, “Ya kamata a fahimci cewa hukumomin nan an tsame su daga biyan haraji daga kudaden aikinssu.

“Amma dokar haraji ta Najeriya ta 2004 ta wajabta musu biyan gwamnatin jihar kudaden harajin da ake cirewa daga albashin ma’aikata da kuma kamfanoni da ’yan kwangilar da ke musu aiki.”