✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan gudun hijirar Baga za su koma gida —Zulum

Gwamnan Borno Babagana Zulum ya ce ranar 26 ga Satumba ’yan gudun hijirar Baga za su fara komawa gida

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya ce ’yan garin Baga da ke gudun hijirar za su fara komawa gida ranar 26 ga Satumba, 2020.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin kaddamar da kwamitin shirye-shiryen mayar da ’yan garin da ke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira zuwa garin nasu da ke Karamar Hukumar Kukawa ta Jihar.

Baga, mai makwabtaka da Tabkin Chadi ya shahara wajen sana’ar kifi, amma yanzu kusan duk jama’ar garin sun yi hijira saboda ayyukan ’yan ta’addan Boko Haram.

Kwamitin mai mutum 23 na karkashin Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’ar jihar, Barista Kaka Shehu Lawan da kuma Babban Sakatare a Ma’aikatar Rayawa, Farfadowa da Sake Tsugunarwa ta jihar, Abba Yusuf a matsayin sakataren kwamitin.

Gwamna Zulum ya ce kaddamar da kwamitin ya biyo bayan wasikar da suka aike wa Babban Hafsan Sojin Sasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai kan bukatar gaggauta sake mayar da ’yan gudun hijirar na Baga daga ranar 26 ga watan Satumbar 2020 zuwa garuruwansu.

Ya ce gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen fitar da kudaden da za a gina muhimman wuraren da aka rusa da hanyoyin Monguno zuwa Kauwa zuwa Baga da kuma samar da tallafin rage radadi ga mutanen.

Ya bukaci kwamitin ya yi aiki tukuru wajen mayar da mutanen gida, yana mai cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta tallafa wa mutanen su sake sabuwar rayuwa.

Da yake tsokaci, shugaban kwamitin, Barista Kaka ya yi alkawarin yin aiki tukuru wajen ganin aikin ya cimma nasara cikin wa’adin da aka dibar musu.