✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Buhari ta fi kowacce rashawa a tarihin Najeriya — Bishop Oyedepo

Ya ce batun yaki da rashawa na gwamnatin Buhari shirin gizo ne kawai

Shugaban cocin Living Faith ta Najeriya, Bishop David Oyedepo, ya ce tun da aka kirkiri kasar, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fi kowacce shahara a tarihin cin hanci da rashawa.

Da yake jawabi a wani taro da aka gudanar a cocin, Bishop Oyedepo ya koka kan halin kuncin da kasar ta fada, wanda ya alakanta da cin hanci.

Ya ce almundahanar da ake zargin dakataccen Akanta Janar da ita kawai ta isa ta warware matsalolin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) da ke gudanar da yajin aiki a yanzu haka.

Ya kuma ce, “Yara da dama na barin karatu saboda rashin kudin da za a biya makaranta, daliban jami’ar ma da tallafi daga al’umma suke iya gamawa.

“Sai ka ga dalibi mai hazaka amma bai da dubu 30 din da zai biya kudin makaranta, saboda son zuciya, da babakeren gwamnatin Buhari,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Zancen yaki da cin hanci da rashawa shifcin gizo ne kawai, domin ba yadda za a yi ka hana abin da a tarihin kasar nan ba shugaban da ya haifar da shi sama da kai”.