✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Ebonyi ta takaita lokutan zuwa wuraren ibada

Umahi ya kuma dakatar da wani waje na gudanar da tarurrukan jama'a a jihar.

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya ba da umarnin takaita lokutan zuwa cibiyoyin ibada zuwa tsawon sa’o’i biyu kacal.

Gwamnan ya kuma dakatar da wani waje na gudanar da tarukan jama’a a jihar.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Fadar Gwamnatin jihar dake birnin Abakiliki.

Matakin gwamna ya biyo bayan sake bullar cutar COVID19 a karo na biyu ne a Najeriya.

Gwamna Umahi ya kuma umarci mataimakin sa, Kelechi Igwe da kwamitin kar-ta-kwana na yaki da cutar a jihar da su tabbatar sun ci gaba da wayar da kan jama’a kan bin matakan kariya.

Ya ce ta hanyar bin matakan ne kawai za a taimaka wa jihar wajen gani ba ta sake samun wani mai dauke da cutar a cikin ta ba.

Kwamitin Kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya kafa domin yaki da cutar dai a kwanakin baya ya zabi gwamna Umahi a matsayin gwarzon gwamna wajen yaki da cutar a fadin Najeriya.