✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Filato ta soke kwangilar aikin hanyoyi uku

Gwamnatin Jihar Filato ta soke aikin kwangilar wasu hanyoyi uku da Kamfanin Gine-Gine na PW yake yi a jihar, saboda yadda kamfanin ya gaza kammala…

Gwamnatin Jihar Filato ta soke aikin kwangilar wasu hanyoyi uku da Kamfanin Gine-Gine na PW yake yi a jihar, saboda yadda kamfanin ya gaza kammala aikin a kan lokaci.

Kamfanin PW, ya yi fice wajen aikin gina hanyoyi da gadoji da filayen jiragen sama da madatsun ruwa a sassan kasar nan.

Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Mista Dan Manjang ne ya bayyana soke kwangilar a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida bayan kammala taron Majalisar Zartarwar Jihar a ranar Laraba.

Kwamishina Manjang ya ce hanyoyin da aka soke kwangilarsu su ne hanyar Shinkwan zuwa Tunkus zuwa Shendam da hanyar Mangu da kuma hanyar Tahos zuwa Ganwuri.

Sai dai Kwamishinan ya kara da cewa nan ba da dadewa ba za a sake bayar da kwangilar aikin hanyoyin.