✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Filato za ta samar wa matasa 20,000 aikin yi a 2022

Gwamnatin jihar ta sha alwashin samar wa matasa 20,000 ayyukan dogaro da kai a 2022.

Gwamnatin Jihar Filato ta tabbatar da shirinta na samar wa matasa 20,000 aikin yi a fadin jihar a 2022.

Ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Danladi Atu, ya fitar a ranar Laraba, a taron masu ruwa da tsaki na jihar.

Ya ce, “Duk ma’aikatun gwamnati, sashe-sashe da cibiyoyi dole ne su yi kokarin sama wa matasa 20,000 aikin yi daga yanzu zuwa 2022.”

Har wa yau, sanarwar ta bayyana yunkurin gwamnan jihar, Simon Lalong, na kammala ayyukan da ya faro kafin karewar wa’adin mulkinsa.

Gwamnatin ta bukaci hadin gwuiwa da sauran kamfanoni masu zaman kansu da ke jihar don bunkasa tattalin arzikin jihar.

An rufe taron da yarjejeniyar samar da hanyoyin dogaro da kai a tsakanin al’umma don rage talauci da rashin aikin yi musamman a tsakanin matasan jihar.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa an shirya taron masu ruwa da tsakin ne don tattauna wasu muhimman abubuwa da suka shafi jihar gabanin shiga shekarar 2022 mai kamawa.