✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Gombe al’ummar Gabukka na neman dauki

Al'ummar yankin na neman samun abubuwan more rayuwa.

Al’ummar kauyen Gabukka da ke yankin Komfulata a Karamar Hukumar Kwami ta Jihar Gombe sun nemi gwamnatin jihar da ta samar musu da abubuwan more rayuwa.

Jauron Gabukka, Malam Munkaila Musa, shi ne ya yi wannan kira a lokacin zantawarsa da wakilinmu, inda ya ce a bangaren abubuwan more rayuwa an bar yankin na Gabukka a baya.

Ya ce suna fama da matsalar rashin hasken wutar lantarki, ba su da tsaftataccen ruwan sha, ba makarantar sakandare kuma babu asibiti.

A don haka dan haka suke kira ga gwamantin Muhammad Inuwa Yahaya da ta duba lamarin kauyensu da idon rahama.

Jauron kauyen na Gabukka ya kara da cewa suna da makarantar firamare guda daya mai azuzuwan karatu hudu amma ba su da karama da babbar sakandare da za su taimaka wa ’ya’yansu wajen zurfafa karatunsu na zamani.

Wasu mazauna garin da muka zanta da su, malam Ya’u Abdullahi da Israfilu Muhammad, sun jaddada rokonsu ga Gwamantin Jihar Gombe, na ganin ta waiwaiyi kauyen Gabukka don share musu hawaye.

Daga nan suka ce kauyen nasu nada dimbim manoma da suke noma amfanin gona mai yawa da ake fita da shi, amma ba su da hanya da za ta saukake musu jigilar kayan.

Kauyen Gabukka na da al’umma fiye da mutum 1,600 da suke rayuwa cikin rashin kayan more rayuwa.