✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Gombe ta fara biyan diyyar rikicin Billiri

Sai dai gwamnatin ta ce tallafi za ta biya, ba diyya ba.

Akalla mutane 524 da rikicin garin Billiri ya shafa Gwamnatin Jihar Gombe ta fara biyan su diyya dan rage musu asarar da suka yi.

A cewar Gwamnan Jihar, Muhammad Inuwa Yahaya, Gwamnatin Jihar ba za ta iya biyan diyya ba, za ta tallafa musu ne domin su samu su rage radadin asarar da suka tafka.

Gwamnan, wanda mataimakinsa Manasseh Daniel Jatauya wakilta, ya ce gwamnati ta ware kimanin Naira miliyan 591 don fara biyan, kuma an kasa tsarin biyan gida biyu.

Ya ce yanzu haka sun fara ne da mutum103 da suka rasa ’yan uwan su ko gidaje da wuraren ibada da kuma wuraren sana’arsu, sannan kashi na biyu kuma za a biya mutum 451 wadanda suka rasa shagunansu da sauran wuraren kasuwanci, kuma za a kammala biyan ne cikin mako guda.

Daga nan sai ya yi fatan ci gaba da zama lafiya da juna, yana mai ba da misali da kasar Ruwanda wacce tayi fama da rikicin kabilanci, amma yanzu ta zauna lafiya fiye da yadda take a da.

A nasa jawabin, Kwamishinan Kudin Jihar, Alhaji Muhammad Gambo Magaji, ya jajantawa al’ummar Billiri sannan ya yabawa gwamnati bisa yadda ta kafa kwamiti aka binciko wadanda rikicin ya shafa domin a tallafa musu.

Ita ma shugabar Karamar Hukumar ta Billiri, Misis Magret Bitrus, ta ce rikicin da ya faru aikin Shedan ne, inda ta yi addu’ar Allah ya kare faruwar hakan a gaba.

Mai Tangle Alhaji Danladi Iliyasu Mai Yamba, ya ce ya bayyana ranar a matsayin ta farin ciki a wajensu saboda yadda gwamnati ta kawo musu dauki kan rikicin.

Ya ce rikicin ya faru ne ba a son kowa ba sai dan sharrin Shedan, amma yanzu komai ya wuce, yana kuma fatan ci gaba da samun dorewar zaman lafiya na har abada a yankin.