✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Gombe za ta fara biyan diyyar rikicin Billiri

An dai kiyasta asarar da aka tafka ta haura miliyan 500.

Majalisar Zartarwar Jihar Gombe ta amince a fara biyan diyya ga wadanda rikicin Billiri ya shafa.

Hakan ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin da gwamnatin Jihar ta kafa don gano musabbabin faruwar rikicin da kuma adadin asarar da akayi.

Kwamitin, wanda aka kafa ranar hudu ga watan Agustan 2021 ya kiyasta asarar da aka yi da cewa ta kai kimanin sama da Naira miliyan 500.

Da yake Karin haske ga manema labarai, Kwamishinan Kananan Hukumomi da Al’amuran Masarautu na Jihar, Ibrahim Dasuki Jalo Waziri, ya ce majalisar ta amince Karamar Hukumar Billiri ta biya kaso 80 cikin 100 na asarar da aka yi ita kuma gwamnatin Jiha za ta biya kaso 20.

Dasuki Jalo, ya ce nan ba da jimawa za a fara biyan diyyar cikin watan Satumba ga wadanda suka yi asarar dukiya sannan iyalan da suka rasa ’yan uwa a rikicin suma za a dube su da idon rahama.

Daga nan sai ya yi kira ga wadanda za a biya diyyar da cewa za a yi hakan ne don tallafa musu ba wai don biyansu asarar da suka yi ba.

Jimillar kudin da aka kiyasta din dai sun kai N591,250.