✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Habasha ta soma kwato garuruwa daga hannun ’yan tawaye

An dai katse hanyoyin sadarwa a yankin na Tigray tare da hana ’yan jarida damar shigarsa.

Gwamnatin Habasha ta ce dakarunta sun yi nasarar kwato garuruwa da dama daga hannun ’yan tawayen TPLF a yankin Tigray.

Gwamnatin ta ce  ta kwato garuruwan Kobo da Woldiya da ke arewacin kasar, bayan kazamin fadan da aka gwabza a yakin da kawo yanzu aka shafe watanni 13 ana yi, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.

An dai katse hanyoyin sadarwa a yankin na Tigray tare da hana ’yan jarida damar shigarsa, abin da ya sa da wuya a iya tantance ikirarin da bangarorin da ke fada da juna ke yi.

A baya bayan nan, hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da tura tawagar masu bincike zuwa arewacin Habasha, domin tantance zarge-zargen aikata laifukan yaki a tsakanin dakarun kasar da mayakan ’yan tawaye, musamman ma kan cin zarafi da ake zargin yi wa mata.

Tun daga karshen watan Oktoba, bangaren gwamnati da na ’yan tawaye ke ikirarin samun nasarar mamaye karin yankuna a arewacin Habasha kamar yadda Rediyon Faransa ta ruwaito.

A ranar Lahadin da ta gabata ’yan tawayen TPLF suka sake kwace garin Lalibela da ke kunshe da wurin tarihi na hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya, kwanaki 11 bayan da dakarun Habasha suka yi ikirarin kwace garin daga hannun ‘yan tawayen.

A watan Nuwamban shekarar 2020 yaki ya barke a Tigray, bayan da Firaminista Abiy Ahmed ya aika da sojoji zuwa yankin da ke arewacin kasar, domin kawar da kungiyar ta TPLF, da ya zarga da kai hare-hare kan sansanonin sojoji.