✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Jigawa ta tura dalibai 210 su karanci Likitanci a Sudan

Ana sa ran su yi aiki a yankunan Jihar da zarar sun dawo.

Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki nauyin dalibai 210 domin karatun aikin likita a kasar Sudan.

Mataimakain Gwamnan Jihar, Umar Namadi ne ya bayyana hakan lokacin da wakilan Kungiyar Editoci ta Najeriya (NGE) suka kai masa ziyara a ranar Laraba.

Umar ya ce makasudin daukar nauyin shi ne don a cike gibin karancin ma’aikatan da Jihar ke fuskanta da kuma inganta harkar lafiya.

A cewarsa, da zarar daliban sun kammala karatun, ana sa ran za su yi aiki a sassa daban-daban na Jihar na tsawon wani lokaci.

“Gwamnatin Jiha ta shirya tura akalla likita guda daya zuwa kowanne asibitin da ke dukkan yankunan karkarar Jihar.

“Daya daga cikin muhimman kudurorin wannan gwamnatin shi ne na tabbatar da samar da ingantacciyar lafiya ga jama’ar Jiharmu.

“A kokarinmu na tabbatar da hakan ne ma ya sa muka fara aikin gina sama da cibiyoyin lafiya 200 a dukkan mazabun Jihar,” inji shi.

Mataimakin Gwamnan ya kuma ce gwamnatinsu ta dauki sabbin matakai wajen ganin ta inganta harkar ilimi a Jihar ta hanyar samar da kayan koyo da koyarwa da kuma bunkasa kwazon dalibai.

Tun da farko Shugaban NGE, Mustapha Isah ya godewa Mataimakin Gwamnan kan irin tarbar da ya yi wa tawagar tasu.

Shugaban Kungiyar, shin ne ya jagoranci mambobin kwamitin shirya taron kungiyar ta NGE yayin ziyarar, gabanin taron da za su yi a Dutse, babban birnin Jihar.

Ya ce ’yan kwamitin kungiyar sun zo birnin Dutse ne gudanar da taronsu, inda ya kuma yaba wa gwamnatin Jihar kan irin ayyukan raya kasar da take aiwatarwa a Jihar.