✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Jigawa ta ware N22bn don aikin tituna

Gwamnatin jihar ta ware kudin ne don sabunta tare da gyara wasu titunan jihar.

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince tare da ware Naira biliyan 22 domin gyara da gina wasu sabbin tituna a fadin jihar.

Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Bala Ibrahim ne, ya bayyana haka a bayan taron majalisar zartaswa na jihar wanda Gwamna Muhammad Badaru ya jagoranta.

Ya ce an amince da Naira biliyan 7.1 don gina hanyar Sule Tankarkar zuwa Amanga, Maitsamiya, Tsugudidi, Santabari da Garin Aiko mai tsawon kilomita 30.5 a watanni 12.

Kwamishinan ya ce majalisar ta kuma amince da gina titin Shuwarin, Wurno, Chamo da Abaya zuwa Isari mai tsawon kilomita 28.9 kan kudi Naira biliyan 6.69.

Majalisar, a cewarsa, ta kuma amince da Naira biliyan 8.1 don gyara titin Yanllema, Kaugama, Kwanar Madana mai tsawon kilomita 37.

“Haka kuma an amince da gyara hanyoyin da suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa a daminar da ta gabata wadanda suka hada da Birnin Kudu, Kiyawa, Jahun, Gambara, Waza, Baranda, Madobi, Darai, Gilima, Gujungu, Hadejia.

“Sauran sun hada da Auyo, Kafin Hausa, Hantsu, Miga, Kwalam, Gilima, Kiri da kuma Majiya,” in ji shi.