✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kaduna ta fitar da sunayen mutanen da ’yan bindiga suka kashe a Giwa

Gwamnatin ta ce ya zuwa yanzu ta gano sunan mutum 29 daga cikin 38 din da aka kashe.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta  bayyana sunayen mutane 29 daga cikin 38 din da ’yan bindiga suka kashe a Karamar Hukumar Giwa da ke Jihar a karshen makon da ya gabata.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da Kwamishinan Tsaro da Al’amura Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya fitar ranar Lahadi.

Kimanin mutune 38 ne ‘yan bindiga suka bi har gida suka kashe a kauyukan Kauran Fawa, Marke da Ruhiya da ke gundumar Idasu a Karamar Hukumar Giwa a ranar Asabar din ta gabata.

Gwamnatin ta ce ta gano sunayen mutane 29 daga cikin wadanda abin ya shafa, yayin da sauran taran  ba a san ko su waye ba, har zuwa lokacin da aka fitar da sanarwar.

Ga jerin sunayen 29 da aka tabbatar kamar haka:

1. Rabi’u Wada
2. Salisu Boka
3. Alh Nura Nuhu
4. Alh Bashari Sabiu
5 Alh Lawal Dahiru
6. Abbas Saidu
7 Inusa Kano
8 Malam Lawal Nagargari
9. Malam Aminu
10. Lawal Maigyad
11. Alh Mustapha
12 Lawal Aliyu
13 Sale Makeri
14 Sani Lawal
15 Auwal Umar
16 Jamilu Hassan
17 Badamasi Mukhtar
18 Malam Jibril
19 Lawal Tsawa
20 Sule Hamisu
21 Sadi Bala
22 Kabiru Gesha
23 Abubakar Sanusi
24 Saiph Alh Abdu
25 Haruna Musa
26 Lawal Hudu
27 Malam Shuaibu Habibu
28 Malam Yahaya Habibu
29 Abubakar Yusuf

Cikin mako guda ’yan bindigar sun kashe mutane da dama a yankunan Kananan Hukumomin Zangon Kataf, Chikun, Birnin Gwari, Igabi da kuma Kauru duk a Jihar ta Kaduna.