✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kaduna ta sake korar malaman makaranta 2,357

Daga cikin wadanda aka kora har da shugabar NUT ta Jihar

Hukumar Kula da Ilimin Bai Daya ta Jihar Kaduna (KADSUBEB) ta ce ta kori malaman makaranta 2,357 sakamakon faduwa jarabawar da ta sake shirya musu a kwanan nan.

Kakakin hukumar, Hauwa Mohammed ce ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwar ranar Lahadi.

Ta ce sun shirya jarabawar ce ga malamai sama da 30,000 a watan Disambar 2021.

Ta ce daga malaman firamare 2,192, ciki har da Shugaban Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT), Misis Audu Amba, aka kora saboda kin zana jarabawar.

Kazalika, ta ce akwai kuma malamai 165 daga cikin 27,662 da suka zana jarabawar da su kuma aka kore su saboda rashin kokari.

“Mun gano cewa ba mu da bukatar dukkan malaman da suka sami kasa da kaso 40 cikin 100 na maki a jawabawar, saboda hakan mun sallame su daga aiki.

“Malaman kuwa da suka sami kaso 75 cikin 100 su ne muka tantance a matsayin kwararrun malamai da suka cancanta su koyar kuma za su fara zuwa kwasa-kwasai kan shugabanci da gudanarwar makarantu,” inji ta.

Da yake mayar da martani kan batun, Shugaban NUT na Jihar, Ibrahim Dalhatu, ya yi watsi da jarawabar da ma korar, inda ya bayyana su a matsayin wadanda aka yi ba bisa ka’ida ba.

Ya ce tuni kungiyarsu ta sami umarnin kotu da ya hana gwamnati shirya jarabawar, amma duk da haka ta yi kunnen uwar shegu da umarnin.

Shi ma da aka tuntube shi, Shugaban NUT na kasa, ya ce suna sane da lamarin, kuma za su zauna ranar Laraba mai zuwa don tattauna batun.

Ko a shekarar 2018 ma, Gwamnatin Jihar sai da ta kori malamai 21,780 da suka fadi jarabawar, sannan ta maye gurbinsu da wasu 25,000.

Bugu da kari, a watan Disamban 2021 ma an sake korar wasu malaman guda 233 saboda amfani da takardun karatu na bogi.

(NAN)