Gwamnatin Kano: Sama da shekara uku ba a biya ma’aikata garatutinsu ba | Aminiya

Gwamnatin Kano: Sama da shekara uku ba a biya ma’aikata garatutinsu ba

Asslam Edita. Ina sake jinjina wa wannan jarida tamu AMINIYA mai albarka. Ina kira ga Mai girma Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje, Khadimul Islam ya ji tsoron Allah ya tuna da ranar tsayuwa a gaban Ubangijin Mai mulki, ya biya ma’aikatan da suka yi ritaya a Jihar Kano garatutinsu. Mutane sun bar aiki, wani shekara daya wani biyu wani uku har yanzu ba a biya su hakkinsu ba. Haba Khadimul Islam ka san irin halin da muke ciki kuwa? Gaskiya dai a tausaya a biya jama’a garatutin nan ko rayuwarsu za ta inganta. Allah Ya kyauta.

 

Daga Idris Mohammed Huguma Takai Jihar Kano, 08099241310Lalata da dalibai: Ga malaman jami’o’i

Assalamu alaikum Edita. Zuwa  ga malaman jami’a da ke yin lalata da dalibai mata. Su sani duk abin da ka yi wa ’yar wani kai ma komai daren dadewa za a yi wa taka. Haba malaman jami’o’i ya kamata ku sani cewa daliban amana ce gare ku da iyayensu suka ba ku domin ku ilimantar da su tare da ba su tarbiyya, amma sai dai kash kun kasa rike wannan amana.Hasali ma maimakon ba su tarbiya, sai sake lalata ragowar tarbiyarsu kuke yi. Don haka kowa ya yi nagari don kansa Allah kuma Yana jiran kowa a madakata.

Daga Hussaini Abba Dambam Dan kishin kasa Karamar Hukumar Dambam, Jihar Bauchi, 08020814173.

 

Kafa Kwalejin Ilimi (FCE) a Malam-Madori

Assalamu alaikum Editan Jaridar Aminiya mai albarka. Don Allah ka ba ni dama in yi kira ga Sanatanmu na Jigawa ta Arewa maso Gabas, Sanata Ibrahim Hassan Hadeja ya taimaka ya kara mika kudirin kafa Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE)  a garinmu na Malam-Madori a gaban Majalisar Dattawa. Mu al’ummar wannan yanki muna bukatar wannan makaranta kuma mun san shi Sanata mai kishin al’ummarsa ne. Wannan makaranta za ta taimaka sosai wajen habaka ilimi da tattalin arzikin Masarautar Hadeja da magance matsalar zaman banza a tsakanin matasa. Daga karshe nake addu’ar Allah Ya sa Shatiman Hadeja ya amsa wannan kira.

Daga Aminu Adamu Malam-Madori, Jihar Jigawa. 08125319709, 08139041679

 

Kalubale ga Gwamnatin Tarayya

Salam Edita. Babban abin bakin ciki shi ne yadda Gwamnatin Tarayya take ikirarin ta kawo karshen Boko Haram, sai ga shi a makon jiya kungiyar Boko Haram ta kwace miliyoyin Naira da kayan abinci da kayan aiki daga hannun sojojin Najeriya da aka dauko daga Damaturu zuwa Biu. Wannan gaskiya abin kunya ne idan aka yi la’akari da yadda Gwamnatin Tarayya take ikirarin gama wa da kungiyar. Ya kamata a binciki al’amarin domin a iya saninmu Gwamnatin Tarayya ta daina biyan albashi da alawus a hannu. Akwai lauje cikin nadi.

Daga Jibril Abba Ocal. 08053932787

 

Ganduje ka tabbatar da kudirin karatu kyauta

Assalam Edita, fatan kana lafiya tare da abokan aiki. Ka ba ni dama in mika sakon jinjina ga Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje, a kan kudirinsa na samar wa da ’ya’yanmu ilimin firamare da sakandare kyauta.

Daga Musa Baban Amina Gala, 08021221518

 

Kira ga Gwamnan Jihar Sakkwato

Assalamu alaikum Edita. Da fatar kana lafiya. Ina kira ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal  ya ji tsoron Allah a kan tsaron Jihar Sakkwato. Domin  ana kashe mutane ba gaira ba dalili saboda haka muna fata Gwamna zai maida hankali don magancewa. Bayan haka ina fata Gwamnan zai cika alkawari na yin hanyar Gada zuwa Dukamaje.

Daga 08128028641

 

Kira ga Gwamnatin Jihar Bauchi

Mu al’ummar kauyen Masussuka da ke Karamar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi muna neman daukin gaggawa domin matsalar zubewar dakuna da zaizayar muhalli. Wallahi, a yanzu sai wanda ya ga halin da jama’a suke ciki. Sannan muna bukatar gyaran asibitinmu na garin Ganji da ke Karamar Hukumar Warji. Babu wurin aiki duk ya lalace.

Daga Hassan Ibrahim Warji. 081218999959

 

Kira ga Gwamnatin Katsina

Assalamu alaikum Jaridar AMINIYA, Allah Ya kara muku daukaka. Ina son ku ba ni dama in yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta Najeriya baki daya ya kamata ku dubi halin da Jihar Katsina take ciki na rashin tsaro. Allah Ya sa mu dace amin.

Daga Muhammadu Musa Dagora 09059678566

 

Rushe masallaci a Fatakwal

Salam Edita, barka da gajiya. A gaskiya yadda gwamnatin Ribas ta rushe massallaci a Fatakwal wannan nuna kabilanci ne. Kuma Shugaban Kasa yas a baki a wannan al’amarin don haka ne ya rataya a wuyan Shugaban Kasa, da sauran shugabanni gaba daya. Dama rikici ya yi yawa a kasa duk dadin kunun  jego ba ya sa mace ta manta zafin haihuwa ba.

Daga Gambo Khashifu Diginsa, Jihar Jigawa 09068054350

 

Jinjina ga Gwamna Masari

Haƙiƙa matakin da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ɗauka na yin sulhu da masu kai wa jiharsa hari yana taka muhimmiyar rawa, lura da cewa Jihar Zamfara da hakan ta samu zaman lafiya.

Daga Isyaku Umar Dagimun, Argungu Jihar Kebbi 08038712889

 

Jinjina ga Babban Hafsan Sojin Sama

Ina mika jinjina ga Shugaban Rundunar Sojojin Sama na Najeriya, Iya Mashal Abubakar Sadik. Mutum ne marar hayaniya, ga sanin ya kamata. Yaransa suna cikin natsuwa saboda hakkokinsu da suke samu a kan lokaci ga muhalli mai kyau.

Daga Kabir Kano, 08037674798

Godiya ga Gwamna Masari

Assalam Mai girma Gwamna Jihar Katsina Aminu Bello Masari, muna yi maka godiya bisa hanyar da ka shimfida mana daga Dayi zuwa Wawar Kaza, ka taimaka mana ka karasa mana zuba Nylon mun gode.

Daga Shu’aibu KT, Musawa Jihar Katsina 08036363753

 

A bai wa jami’an tsaro hadin kai

Ina kira ga jama’a su rika bai wa jami’an tsaro hadin kai domin samun mafita kan masu garkuwa da jama’a a sassan Jihar Katsina. Ita kuma gwamnati ta ci gaba da daukar dukkan matakan da suka kamata domin samun sauki,.Allah Ya kawo mana mafita, amin.

Daga Saminu mayentea Batsari, 08036773485

 

Godiya ga asibitin Bawo Clinic

Assalam Edita. Don Allah ina so ka ba ni dama in mika godiya ta musamman ga hukumar asibitin nan mai zaman kansa da ke Daura wato Asibitin Bawo Clinic, inda aka yi mini tiyata a asibitin a ranar 6-8-2019. Hakika an yi mini abubuwan karramawa sosai kuma har akwai magunguna da aka ba ni kyauta wadanda ba a cikin kudin aikin suke ba. Alhamdu lillahi babu abin da zan ce sai Allah Ya saka musu da alheri Allah Ya biya su, Allah Ya kara musu basira, Allah Ya sa a gama lafiya amin.

Daga Hadi Tsohon Sarki Daura, 08164205067, 07015256836

 

Ga Ministar Jinkan Jama’a

Edita don girman Allah a ba ni fili in taya murna ga Minista Sa’adiya Umar Faruk, sannan in nusar da ita cewa aikinta ya fi na kowane Minista yawa da muhimmanci. Kada ta manta, ba bangare guda aka ba ta ba, aikinta ya shafi kowane bangare kuma ya shafi dukkan ’yan Najeriya. Don haka ta tsaya ta yi dogon bincike wajen zaben abokan aikin da za su taimaka mata  don samun nasara. Ina yi miki addu’ar Allah Ya ba ki ikon sauke nauyin da Baba Buhari ya ba ki da gagarumar nasara,

Daga Amiru Isah Bakori, 07068147933

 

A karbar mana hakkinmu daga barayin gwamnati

Ya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari! Yadda ake karbar kudi daga barayin gwamnati, to mu ma sallamammun ma’aikatan NITEL da ’yan fansho a karbar mana hakkinmu daga wadanda suka rike mana.

Daga Ibrahim Dankoli, Jada, Jihar Adamawa, 07034542318.

 

Kira ga kungiyoyin kare hakkin yara da nakasassu

Assalamu alaikum Edita. Zuwa ga kungiyoyin kare hakkin yara da nakasassu su sa ido ga matan da ke dauko yara kanana daga kauyukan Arewa suna kai su Kudu domin yin musu bara suna karbewa ba sa sa su a makaranta. Haka guragu kanana ake dauko su daga kauyuka ana zuwa da su Kudu ana lalata musu rayuwa ba tarbiyya ba ilimi.

Daga Abdullah Shehu Mokola Ibadan Jihar Oyo, 08104410660

 

Fatar alheri ga Gwamna Talamiz

Assalam Edita, ka isar min da sakon fatar ga Gwamna Badaru Abubakar Talamiz na Jihar Jigawa. Ya kara jajircewa wajen ayyukan da yake yi a jiharmu Ya Allah Ya ba shi sa’a.

Daga Ahmed Ghali 09054986613