✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta dauko Manyan Lauyoyi 4 kan Abduljabbar

Kotu ta mayar da Abduljabbar gidan jari.

Gwamnatin Jihar Kano ta dauki Manyan Lauyoyi (SAN) guda hudu domin gurfanar da Sheikh Abduljabbar Kabara a gaban kotu kan zargin sa da batanci ga Manzon Allah (SAW).

A ranar 16 ga Yuli, 2021 Gwamnatin Jihar Kano ta fara gurfanar da Abduljabbar Kabara kan zargin batanci ga Manzon Allah (SAW) da tunzura jama’a da dangoginsu.

A ci gaba da zaman Babbar Kotun Mausulunci da ke zamanta ga Kofar Kudu a birnin Kano ne Suraj Sa’eda (SAN), wanda ya jagoranci sauran manyan lauyoyin uku ya sanar da wakilcin da suke yi wa gwamnatin jihar.

Suraj Sa’ed (SAN) ya bukaci kotun ta karbi sabbin tuhume-tuhumen da gwamanti take wa malamin ta yi watsi da na farkon, ya kuma nemi a saurari zarge-zargen kafin a ji daga bangaren wanda ake kara.

Amma lauya mai kare Abduljabbar Kabara, Saleh Muhammad-Bakaro, ya ce lauyoyin da suka wakilci Antoni-Janar na Jihar Kano ba su da hurumin bayyana a gaban kotun

Muhammad-Bakaro ya ce, “Manyan Lauyoyin Najeriya ba su da hurumin bayyana a gaban kotun Shari’ar Musulunci.”

Muhammad-Bakaro ya bukace kotun ta yi watsi da sabbin tuhume-tuhumen, saboda a Shari’ar Musulunci ba a sauya tuhuma idan aka gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu bisa Sashe na 2, 108 da 126(a) da Dokar Manyan Laifuka na 2019.”

Daga nan alkalin kotun, Mai Shari’a Abdullahi Sarki Yola ya daga sauraran shari’ar zuwa ranar 2 ga Satumba, 2021 ya kuma sa a ci gaba da tsare malamin a gidan yari.

Bayan zaman kotun, daya daga cikin Manyan Lauyoyin, Farfesa Lawan Mamman Lawan (SAN), ya shaida wa ’yan jarida cewa hujjojin bangaren wanda ake kara suka gabatar masu rauni ne.

Amma bangaren wanda ake zargi sun kawo maganar hurumi, wanda idan aka dauko shi, sai kotu ta yanke hukunci a kai kafin a shiga cikin batun.

Sagir Kano Saleh da Lubabatu I. Garba da Salisu Ahmad, Kano.