✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta fara kwace filaye marasa takardu don gina makarantu

Za a gina katafarun makarantu a filaye da gine-ginen da za a kwace.

Gwamantin Jihar Kano ta fara kwace filaye da gine-gine marasa cikakkun takardu domin gina manyan makarantu a birin Kano.

Gwamnatin ta ce za ta gina katafarun makamarantu a filaye da gine-ginen ne domin rage cunkoson dalibai, musamman ganin yadda matsalar tsaro ke addabar jihohin da ke makwabtaka da Jihar Kano.

“Duba da matsalar tsaro a jihohin da ke makwabtaka da Jihar Kano da kuma cunkoson dalibai a makarantun da ke wajen garin Kano, Gwamantin Jihar Kano ta fara kwace filaye da gine-gine da aka mallaka ba bisa ka’ida ba da kuma marasa cikakkun takardu a birnin Kano domin gina katafarun makarantun sakandare,” inji Kwamishinan Yada Labaran Jihar Kano, Muhammad Garba.

Ya kara da cewa, “Manufar yin hakan ita ce rage cunkoson dalibai a makarantun kwana da ke kananan hukumomi 36, duba da yawaitar garkuwa da ake yi da dalibai a makarantun kwana a jihohin da Jihar Kano take makwabtaka da su.”

Da yake sanar da hakan a ranar Litinin, kwamishinan ya ce gwamnatin ta riga ta kwace gine-ginen da ke Filin Bola a kan Titin Kotu da ke Karamar Hukumar Tarauni, saboda mai shi ba shi da izinin fara gini; Saboda haka gwamnati za ta gina babbar makaranta a kan filin.

A cewar kwamishinan, gwamnatin jihar na sake nazarin yanayin tsaro, ganin yadda ake fatattakar ’yan bindiga da dangoginsu a dazukan jihohi masu makwabtaka da jihar ta Kano.

Amma a matsayin matakin wucin gadi, gwamnatin za ta fara da tabbatar da samun isasshen tsaro a makarantu.