✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta kama mabarata 500

“In har ina nan a matsayin Kwamishiniya a Kano, to tabbas sai na kawo karshen bara a titunan.”

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da kame mabarata kimanin 500 da suka addabi jihar da gararanba a titunan da sunan bara.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Kwamishiniyar Harkokin Mata ta jihar, Dokta Zahra’u Muhammad-Umar a ranar Juma’a.

A cewarta, daga cikin wanda aka kama akwai mata da maza da yara da almajirai da kuma yaran ba sa zuwa makaranta kuma ba su da abincin ci.

Kwamishiniyar ta ce matakin kamen na daga cikin irin tsare-tsaren gwamnatin jihar wajen ciyar da rayuwarsu da ta Kano gaba.

“Mun fahimci cewa ana samun marasa da’a da cikinsu da yawa.

“Za mu ci gaba da kame su domin mu tsaftace titunan Kano, da kuma kauda matsalar tsaro,” cewar Kwamishiniyar.

Dokta Zahra’u ta kuma ce daga cikin mabaratan da aka kama har da wata tsohuwa mai kimanin shekaru 70 dauke da taba sigari a cikin kayanta.

“Irin wadannan mata za su iya lalata tarbiyyar yaranmu.

“Yin bara a tituna na iya shafar rayuwar yaranmu, musamman idan muka dauki almajiri yana yi mana aikin gida,” in ji Zahra’u.

‘Duk mabaracin da muka sake kamawa a karo na biyu kotu za mu ka shi’

Ta jinjina wa Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje kan yadda yake tallafa wa ma’aikatar kan rayuwar mabaratan.

“Mun dauki sunayensu, adireshi, lambar waya, sannan muka mayar da su ga jihohinsu na asali tare da alkawarin tallafa musu.

“Wadanda suka fito daga makwabtan jihohi, za a rubuta yarjejeniya da mai unguwar da suke cewa za a aike da su kotu matukar aka sake kama su a karo na biyu.”

Kwamishiniyar ta kara da cewa Gwamnatin Jihar za ta mayar da hankalinta wajen kawar da masu talla a kan tituna, musamman yara mata.

Ta ja hankalin jama’ar jihar da su ci gaba da rike yaransu a gida don su zama abin koyi a nan gaba.

‘Sai na kawo karshen bara a Kano’

“In har ina nan a matsayin Kwamishiniya a Kano, to tabbas sai na kawo karshen bara a titunan Kano,” cewar Dokta Zahra’u.

Kazalika, ta ce Ma’aikatarta ta zata mayar da almajiran da suke a makwabtan jihohi, musamman wanda suke bara don neman abin da za su ci.

Ta ce tuni gwamnati ta tattauna da malam tsangayu kan hana almajiran ci gaba da bara a kan titiuna la’akari da irin illolin da take tattare da su.