✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta musanta cin zarafin yara a gidan marayu

Kwamishinar ta musanta zargin da wasu mata biyu suka yi a gidan rediyo.

Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da rahoton zargin cin zarafin yara da wasu jami’anta suka yi a gidan marayu da ke Nassarawa a jihar.

Kwamishinar Harkokin Mata da Ci Gaban Al’umma ta jihar, Dakta Zahra’u Muhammad Umar, ta yi watsi da rahoton yayin da ta zanta da manema labarai a ranar Lahadi.

“Wasu masu yin barna ne suka hada labarin don bata sunan gwamnatin jihar nan.

“Amma abin da ta faru shi ne ba mu da hurumin ci gaba da zama da kuma kulawa da yaran da suka haura shekara 18 a gidan marayu. Doka ma ba ta ba mu wannan damar ba.

“An bukaci wasu mutum biyu, Ladidi da Saudat da su bar gidan marayun tun da yanzu sun zama manya.”

Ta bayyana cewa matan biyu, wadda daya daga ciki bazawara ce, dayar kuma na da aure har da ’ya’ya uku, sun ki barin gidan sannan sun shiga yi wa kwamishinar bita da kulli da sauran ma’aikatan don bata musu suna.

“Sun shiga gidan rediyon sun yi kazafin cewar ana cin zarafin yara, ana kai su wurare daban-daban ba bisa ka’ida ba.”

Ta ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti wanda ya gudanar da bincike sannan ya gano zargin karya ne, inda ta ce kwamitin ya yanke shawarar cewa Ladidi da Saudat su bar gidan saboda sun haura shekara 30.

“Lokacin da na zama kwamishina, na tausaya wa manya, na zama uwa gare su, na sanya wasu daga cikinsu a manyan makarantu.”

Ta ce gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na daukaka darajar rayuwa a tsakanin ‘yan kasa ta hanyar manufofi da tsare-tsare.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin binciken, Alhaji Kabiru Zubairu, ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ya kunshi mambobi tara da za su kula da yadda ake kulawa da marayun.

Kwamitin ya hada da Jami’in ‘yan Sanda a matsayin Sakatare, REPA, Darakta (Yaron Ma’aikatar), Masanin Ilimi daga Ma’aikatar Ilimi, Jami’in Shari’a, Likita da Jami’an Jin Dadin Jama’a a matsayin mambobi.

Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya ruwaito cewa an kafa gidan marayu na Nassarawa a shekarar 1960, wanda a halin yanzu yana dauke da yara sama da 300 da ake dawainiya da su.