✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta rage kudin rajistar masu A Daidaita Sahu

Gwamnatin jihar ta rage kudin sabunta rajistar zuwa N5000.

Matuka baburan A Daidaita Sahu da Gwamnatin Jihar Kano sun cimma matsaya kan takaddamar kudin sabunta rajistar lambar baburan, wanda ya kai ga matukan tsunduma yajin aikin kwana uku.

Taron cimma matsayar wanda ya shafe tsawon awa shida a ranar Laraba, ya samu halartar lauyoyin kungiyar matuka baburan da kuma wakilin hukumar KAROTA, mai kula da zirga-zigar ababen hawa a jihar.

An cimma matsaya tare da rage kudin sabunta rajistar daga N8,000 zuwa dubu N5,000, yin sabon rajista kuma N12,000 maimakon N18,000 da aka bayyana da farko.

Sai dai Shugaban Hukumar KAROTA, Baffa Babba DanAgundi, ya ce duk wanda ya gaza biyan kudin sabunta rajistar, zai biya kudaden da aka bayyana tun asali, wato N18,000 ga mai yin sabuwar rajista da kuma dubu N8000 ga mai sabuntawa.

Idan ba a manta ba a satin da ya gabata ne matuka baburan na A Daidaita Sahu a Jihar Kano suka shiga yajin aikin kwana uku, lamarin da ya tsaida harkokin yau da kullum a fadin jihar.