✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta rufe cibiyoyin lafiya 5

Cibiyoyin lafiya da aka rufe suna aiki ba bisa ka'ida ba.

Gwamnatin Kano ta rufe wasu cibiyoyin kula da lafiya masu zaman kansu guda biyar kan rashin sabunta lasisin aikinsu a Jihar.

Hukumar Kula da Asibitoci Masu Zaman Kansu ta Jihar Kano (PHIMA) ta rufe cibiyoyin ne a unguwannin Kabuga da Janbulo, duk a Karamar Hukumar Gwale ta Jihar.

Babban Sakataren Hukumar, Dokta Usman Tijjani Aliyu ya ce, “Hakan na daga cikin aikin da suke yi na tabbatar da bin doka da kuma ganin dukkannin cibiyoyin lafiya da ke Jihar Kano sun sabunta rajistarsu da PHIMA”.

Ya sanar a ranar Alhamis cewa wuaren da aka rufe din su ne Fairuz Islamic Chemist, Gara Beauty Salon, Islamic Barbing Salon, Tal’udu Barbing  da kuma Rumfar Shehu Barbing Salon.

Dokta Usman Aliyu ya ce cibiyoyin za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an kammala yin duk abin da ya kamata da hukumar.

Ya kuma yi kashe cewa duk wata cibiyar lafiya ko mutum da aka gano yana aiki ba bisa ka’ida ba a jihar zai yaba wa aya zaki.