✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta rufe makarantu

Ganduje ya umarci iyayen su kwashe 'ya'yansu da ke makarantun kwana

Gwamnatin Kano ta ba da umarnin rufe daukacin makarantun da ke jihar nan take.

Kwamishinan Ilimin Jihar, Muhammad Sanusi Kiru ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje ya amince da rufe makarantun ne a ranar Talata.

Sanarwar ta bukaci iyayen da ‘ya’yansu ke makarantun kwana da su shirya dawo da yaran gida ranar Laraba, 16 ga watan Nuwamba, 2020.

Kwamishinan Ilimin bai bayyana dalilin gwamantin jihar na daukar matakin rufe makarantun ba.

Sai dai a baya-bayan nan gwamnatin ta bayyana damuwa game da karuwar masu kamuwa da cutar coronavirus a jihar.

Sakamakon haka ta bukaci ma’aikatan yaki da da cutar su dawo bakin aiki.

Matakin na Jihar Kano na zuwa ne washegarin ranar da Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauki makamanciyarta ta rufe makarantu daga ranar Laraba, 16 ga Nuwamba, 2020.

Kaduna ta ce ta yi hakan ne domin dakile yaduwar cutar COVID-19 da yaduwarta ke hauhawa a jihar.

A Jihar Katsina mai makwabtaka da jihohn biyu kuma mahara sun kai hari a makarantar GSSS Kankara  inda suka yi garkuwa da daruruwan dalibai.

Kungiyar Boko Haram, ta wani sakon sauti da shugabar, Abubakar Shekaru ya fitar ta yi ikirarin garkuwa da daliban na Kankara.

A yammacin ranar ta Talata ce Gwamantin Jihar Zamfara mai ta rufe makarantunta guda 10 a yankunanta masu iyaka da jihohin Katsina da Kaduna.

Ta ce ta yi hakan ne duba da abin ya faru ranar Juma’a na garkuwa da daliban na Kankara.