✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta sallami wasu ma’aikata kan zargin cefanar da filaye

Gwamnatin Jihar ta sallami ma'aikatan kan zargin cefanar da wasu filaye mallakinta.

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da sallamar wasu ma’aikatan Hukumar Kasa da Safiyo ta Jihar, bisa zarginsu da laifin yin takardun jabu tare da sayar da wasu filaye mallakin hukumar.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran Jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce kwamitin bincike da aka kafa wa ma’aikatan ya gano cewa ma’aikatan sun yi amfani da takardun bogi da kuma sayar da filayen gwamnati wanda hakan ya saba da dokar aikin gwamnatin jihar karkashin lamba ta 04406.

Ma’aikatan da abin ya shafa sun haɗa da Abdulmuminu Usman Magami, mai matakin albashi na 6 da Abdullahi Nuhu Idris mai matakin albashi na 10 da kuma Audu Abba Aliyu mai matakin albashi na 05.

Sauran wanda da abin ya shafa ya hadar da Baba Audu mai matakin albashi na 13.

Daga karshe sanarwar ta ja hankalin ma’aikatan gwamnatin jihar da su kasance masu bin doka da oda.