✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta soke lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu da ke Jihar

Gwamnatin ta ce dole ne a sake tantance dukkan makarantu masu zaman kansu da ke Jihar.

Gwamnatin Jihar Kano ta ba da umarnin dakatar da lasisin dukkanin makarantu masu zaman kansu da ke fadin Jihar, har sai an sake tantance su.

Kwamishinan Ilimin Jihar, Sanusi Sa’id Kiru ne ya shaida wa manema labarai hakan a Kano, ranar Litinin.

Sai dai Kwamishinan ya ce daliban makarantun za su ci gaba da zuwa har zuwa lokacin da za a kammala tantancewar.

Hukuncin na zuwa ne yayin da aka gurfanar da mai makarantar ‘Noble Kids’ a kotu, wanda ake zargi da kisan Hanifa Abubakar, mai shekara biyar a makarantarsa.

Kwamishinan ya ce za a kafa wani kwamiti na musamman da zai tantance makarantun sannan za ta fitar da matakan da za a yi amfani da su wajen tantance makarantun baki daya.

Kazalika, ya ce dukkan makarantun da ba su cika sabbin ka’idojin da za a saka ba, za a rufe su na dindindin.

Tun bayan cafke wanda ake zargi da kashe Hanifa, lamarin ya ta da hazo tare da saka fargaba a zukatan dubban iyayen da ke kai ’ya’yansu makarantu masu zaman kansu.

Tuni dai al’ummar Jihar suka tofa albarkacin bakinsu kan matakin na Gwamnatin Jihar.